Zaman Lafiyar Najeriya Shine Afuwa Da Daukar Nauyin ‘Yan Bindiga – Gumi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shahararren malamin addinin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ?ara jaddada matsayarsa cewa yi wa yan bindiga afuwa da ?aukar nauyin su ne ka?ai hanyar kawo ?arshen zubar da jinin mutane a Arewa.

Malamin ya yi wannan furuci ne a wurin sanya marayu rukuni na uku a shirin samar musu da ilimi, kula da lafiya kyauta, wanda gidauniyar musulunci a Kawo ta ?auki nauyin shiryawa.

Sheikh Gumi ya shawarci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari, kada ta zama silar ?arin kashe-kashen mutane, ta hanyar kuskuren da take kokarin yi na ayyana ‘yan Bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Malam Gumi yace: “Idan har akwai wata hanya da zata dakatar da zubar da jini, zai fi kyautuwa a yi musu kwatankwacin abinda aka yi wa maya?an Niger Delta.” “Sun kasance suna fasa bututun mai da zubar jinanen mutane, amma aka yi musu afuwa suka aje makamansu idan za’a musu afuwa da ?aukar nauyinsu, inaga za’a iya yi wa yan bindiga haka.”

“Mun gana da su kuma a shirye suke su aje makamansu. Amma idan sun daina kuma ba’a samar musu da ilimi ba, da ku?in da zasu kula da kansu, zasu koma gidan jiya ne.”

Related posts

Leave a Comment