Sama Da Mutum Miliyan 6 Ba Su Katin Zabe Ba – INEC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a daidai lokacin da ya rage kwana guda a fara gudanar da za?en shugaban ?asa na 2023, hukumar za?e mai zaman kanta INEC na ci gaba da bayyana shirye-shiryenta na gudanar da za?en.

Cikin wani sa?o da ta wallafa a shafinta na Twitter INEC ta ce ya zuwa yanzu mutanen da suka kar?i katinsu na za?e na din-din-din, sun kai miliyan 87, da dubu 209 da 7.

Ta kuma ce akwai mutum miliyan 6, da dubu 259, da 229 su ne adadin wa?an da ba su kar?i katin nasu ba ya zuwa yanzu.

Jumillar adadin wa?anda suka yi katin za?en a Najeriya ya kai miliyan 93, da dubu 468,da 236.

Cikin jadawalin ta bayyana yawan katunan da kowacce jiha ta kat?a da wanda ba a kar?a ba da kuma kashi nawa ta karba cikin 100.

A Najeriya dai ana yi wa wannan za?en kallon mai cike da ?alubale, ganin matsalolin da ?asar nan ke fama da su da suka ha?a da na tsaron da tattalin arzi?i da dai sauransu.

Related posts

Leave a Comment