Mun Bankado Shirin ‘Yan Siyasa Na Amfani Da Kudi Wajen Sayen Kuri’u – EFCC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ?asa Abdulrasheed Bawa, ya ce ‘yan siyasa na rike da sama da N500bn na tsofaffin ku?i wanda ba a kai ga mayar wa Babban Bankin ?asar ba.

Abdulrasheed Bawa ya bayyana hakan ne a wani shiri na gidan talabijin na Channels na siyasar mu a yau.

Ya ce hukumar ta samu bayanai da ke nuna cewa ‘yan siyasa na shirin amfani da wasu hanyoyi na sayan kuri’a lokacin za?e.

“’Yan siyasa basu da wata mafita a yanzu illa ta sayan kuri’u saboda sun ga na’urar tantance masu za?e ta BVAS za ta kawo musu cikas.

Wannan bayanan sirri ne da muka samu. Sai dai, ina farin cikin cewa dukkan hukumomin tsaro na aiki tukuru wajen ganin an gudanar da za?en lami lafiya,” in ji Bawa.

Shugaban na EFCC ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su bai wa kungiyar ha?in-kai a ?o?arinta na yaki da masu sayan kuri’a a za?en Shugaban ?asa da na ‘yan Majalisar Tarayya da za a gudanar ranar Asabar.

Ya kuma bu?aci ‘yan ?asar da su za?i mutane masu dattako da sanin ya kamata a za?en da ke tafe.

A cewarsa, sayan kuri’a babban batu ne da ke shafar makomar Najeriya da kuma ‘yan ?asar, don haka ya kamata a dakatar da hakan ta kowace hanya.

Related posts

Leave a Comment