Hukumar kula da Ilimi (SUBEB) tace kimanin Yara 775,000 suka bar zuwa makaranta saboda rashin tsaro a gaba daya kananan Hukumomi guda 34 da muke dasu a Jihar.
Direkta na Wannan Hukuma,Abdulmalik Bello,ya bayyana ma manema labarai cewa hare haren yan bindiga da annobar Corona (COVID-19) shine sila a ranar Laraba a wani gangami akan komawa Makaranta da akayi.
Kamar yanda Bello yace,kananan Hukumomin Kankara da Kafur suke da lamba mafi yawa ta Yaran da suka daina zuwa Makaranta a Jihar.
Ganganmin da yasamu hadin gwuiwar (UNICEF),Foreign Commonwealth and Development office (FCDO) ce ta dauki nauyin shi.
A bayyanin shi, Bello yace a shekarar 2018 adadin Yaran da suka bar zuwa Makaranta 1,137,000. Da jajircewar da kokarin Gwamnati da hadin guiwar UNICEF da UBEB, Yara 360,000 a cikin su yanzu sun koma Makaranta.
Ya kara da cewa Hukumar,da hadin guiwar abokan aiki masu son cigabanta suna buri da fatan wasu Yara 200,000 da suka bar Makaranta su koma Makaranta ta hanyar gangami da akeyi akan komawa Makaranta.
Bello yace: “Idan akayi la’akari da sakamakon kidaya da akeyi duk shekara a Makarantu,a yanzu muna da fiye da Yara 775,000 da suka bar Makaranta.
