A yayin da ake cigaba da bukukuwan Babbar Sallah ta bana, kungiyar ‘yan kasuwar arewacin Najeriya ta kira yi al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan lokacin na Sallah wajen hadin kai da yin addu’o’in wanzar da zaman lafiya a fadin ?asa baki daya.
Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwa na Arewacin Najeriya kuma Galadiman cika soron Adamawa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a zantawarsa da wakilinmu a Yola.
Alhaji Ibrahim yace lokacin bukukuwan Sallah yana da mutukan muhimmanci ga Al’umma Musulmi saboda damace ga al’ummar musulmi da su gudanar da ayyukan cigaban addinin musulunci da musulmi baki daya.
86 ya kuma shawarci ‘yan kasuwa dake arewacin Najeriya da su kasance masu hada kansu da kuma gudanar da kasuwancinsu bil hakki da gaskiya wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban harkokin kasuwancinsu yadda ya kamata.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwan na Arewacin Najeriya ya kuma taya al’umma Musulmi murnan bikin Babbar Sallah tare da shawartar Musulmi da su kasance masu ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki da kuma taimakawa marassa galihu domin naman tsira ranan gobe kiyama.
Harwayau Ibrahim 86 ya mika gaisuwar Sallah ga daukacin ‘yan kasuwa dake fadin Najeriya, tare da shua’gabanni, da ma sarakunan gargajiya da dai sauransu.
Ya kuma jaddada kiransa ga Al’umma musamman wadanda suka cancanci yin rijistan katin zabe da su gaggauta zuwa cibiyar rijistan katin zaben domin a cewarsa hakan ne zai bada daman za?ar shugabanni da suke so.
