Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugaban kasa ?ar?ashin Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya za?i tsohon gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban ?asa.
Tinubun ya bayyana haka ne ga ?an jarida a garin Daura yayin wata ziyarar barka da Sallah da ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A kwanakin baya ne dai Tinubun ya ?auki Ibrahim Masari a matsayin mataimaki duk da tun a lokacin ana ta ce-ce-ku-ce kan cewa na ri?o ne, kuma shi ma Masarin a yayin wata hira da BBC a kwanakin baya ya tabbatar da cewa a shirye yake ya bar kujerar idan aka samu wanda ya fi shi cancanta.
Tinubun ya bayyana cewa duk da bai tattauna wannan batu da Kashim Shettima ba amma ga shi ya bayyana wa ?an jarida.
Kashim Shettima dai a halin yanzu shi ne Sanata mai wakiltar yankin tsakiya na Jihar Borno.
Haka kuma Shettima ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a ya?in neman za?en Tinubu a lokacin za?en fitar da gwani na Jam’iyyar APC
