Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah da ‘yar kwallon Chelsea, Sam Kerr sun lashe kyautar fitattun ‘yan wasa ta bana ta PFA.
‘Yan wasan biyun sun lashe kyautar takalmin zinare a kakar da aka kammala a gasar Premier ta 2021-22 da kuma gasar mata ta Super League.
Dan wasan Manchester City, Phil Foden, mai shekara 22 shi ne gwarzon matashi da ‘yan wasan suka zaba a bana, karo biyu a jere kenan.
Lauren Hemp, mai shekara 21, wadda take taka leda a City, ita ce mace matashiya da aka zaba ba kamarta, kuma karo hudu a jere.
Hakan ne ya sa ‘yan wasan tawagar Ingila ta zama ta farko da ta lashe kyautar ta PFA da yawa a tarihi.
Salah dan kasar Masar ya zama na shida da ya karbi kyautar PFA karo biyu, bayan Mark Hughes da Alan Shearer da Thierry Henry da Gareth Bale da wanda ya lashe a bara Kevin de Bruyne.
Salah ya ci kwallo 24 a gasar Premier League da aka kammala a bana, iri daya da yawan wadda Son Heung-min ya ci a kakar da ta kare.
Dan kasar Masar ya bayar da kwallo 14 a ka zura a raga ya kuma dauki Carabao Cup da FA Cup a Liverpool.
