Kano: An Damke Mutumin Da Ya Gina Gida Da Shafukan Alkur’ani

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Hukumar Hisbah mai tabbatar da bin dokokin Shari’ar Musulunci a Jihar ta ce ta kama mutum uku da ake zargi da yin amfani da shafukan Al-?ur’ani mai girma wajen gina wani gida a unguwar Gaida da ke jihar.

Mataimakin kwamandan hukumar mai kula da ayyuka na musamman na, Ustaz Usaini Usman Cediyar ‘Yan-?uda, ya fa?a wa BBC Hausa sun kama mai gidan tare da malamin da ake zargin shi ne ya sa shi amfani da shafukan wajen yin gini.

Ya ?ara da cewa a lokacin da jami’ansu suka isa wurin da ake ginin sun tarar da wasu daga cikin takardun ?auke da rubutun wani ?angare na ?ur’ani.

“Tuni mutanen unguwar suka yi gaban kansu suka rushe ginin,” a cewarsa.

Sai dai ya ce wadanda ake zargi sun shaida musu cewa suna amfani da shafukan ne a wajen yin ginin saboda tsaro.

Related posts

Leave a Comment