Gaskiya Nake Gayawa Gwamnati Ba Adawa Ba – Sheikh Nuru Khalid

Mashahurin Malamin addinin Musulunci Sheikh Nuru Khalid ya bayyana cewar ko kadan ba adawa da gwamnatin Buhari ce tasa yake yawan sukan tsare-tsaren ta ba, sai dai kawai tsagwaron gaskiya da yake fadi ne.

Malamin ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da sashin Hausa na gidan rediyon BBC Hausa ya yi dashi akan tarihin rayuwar sa.

Shehin malamin wanda shine limamin Masallachin juma’a ne a birnin tarayya Abuja Abuja, ya ?ara da cewar ba abu bane wanda za’a lamunta yawaitar zubar da jinin jama’a da ake yi a wannan gwamnati, ya zama dole a fito ayi bayani da babbar murya cewa gwamnati ta gaza ta wannan fanni.

Sheikh Nuru Khalid ya bayyana cewar babban nauyin dake rataye akan kowace gwamnati shine tsare rayuka da dukiyoyin jama’ar data mulka, dukkannin gwamnatin da ta gaza ta wannan fanni to ba ta da wani amfani ga jama’arta.

Related posts

Leave a Comment