Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Tijjani Ramalan Shugaban Tashocin ‘Yanci Na Liberty ya wa Gwabna Kaduna Sanata Uba Sani da Iyayen Yara Jaje sace ?alibai 287 a Kaduna
Ramalan ya yi tir da garkuwa da ?aliban sakandare 287 a garin Kurebe, cikin ?aramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna da fatan Jami’an Tsaro kasa za su Gaggauta ceto su.
Shugaban tashoshin ‘yancin ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar wadda aka rarraba wa manema labarai a Abuja.
“Abin takaici ne da ba?in ciki yadda matsalar tsaro ke cigaba da lalacewa a Najeriya musamman yankin arewa muna kira da babbar murya ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su yi dukkanin mai yiyuwa domin ceto yankin daga durkushewa”.
