Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewa i?iraarin da Kungiyar ?ungiyar Afuwa ta Duniya, ‘Amnesty International’ ta yi a ranar Juma’a, ta tabbatar da cewa sama da mutane 400 yara da manya masu gudun hijira ne Boko Haram suka arce da su, ba 200 ba, kamar yadda rahotonnin farko su ka bayyana.
An sace su ne daga sansanin gudun hijira daban-daban, a Gamboru Ngala, Jihar Barno a cikin wannan makon.
Shugaban ?asa Bola Tinubu ya tabbatar da sace masu gudun hijirar, amma bai bayyana adadin yawan su ba.
Amnesty International dai ta ce ?aruruwan wa?anda aka sacen sun fito ne daga Babban Sansani, Zulum, Sansanin Arabic duk a yankin Gamboru.
A ranar Alhamis Gwamna Babagana Zulum ya ce gwamnati ba ta tantance yawan adadin wa?anda aka arce da su ?in ba, kamar yadda jaridar HumAngle ya ruwaito.
An sace mutanen da suka ha?a da mata da ?ananan su 400, rana ?aya da ?aliban firamare da na sakandare 287 da aka sace a Kuriga, cikin ?aramar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
“Sace mutanen nan da Boko Haram suka yi a baya-bayan nan, hakan ya nuna ?arara cewa Shugaban ?asa Bola Tinubu da gwamnatin sa ba su da wani kyakkyawan shirin magance wannan gagarimar matsalar tsaro.”
Yayin da AI ta yi Allah wadai da wannan garkuwa da mutum sama da 600, ta kuma ce hakan ya nuna yadda Boko Haram suka sake darkakowa da ?arfin su.
?ungiyar ta ce gwamnati na ci gaba da nuna cewa gagarimin aikin kare lafiya, dukiyoyi da rayukan jama’a ba ya gaban wannan kwamiti.
Haka kuma ?ungiyar ta Afuwa ta Duniya ta ce ya kamata a ri?a ?ora laifin it n wannan ?arna a kan kwamandojin da tsaron yankin da abin ya faru a duk lokacin da aka kai farmaki a yankin da suke tsaro.
Wannan gagarimar garkuwa da mutane a Kaduna da Barno, ta zo ne kwana biyu kacal bayan Ministan Tsaro Muhammad Badaru ya fito fili ya bayyana cewa rashin isassun sojoji ne ke sa mahara da ‘yan bindiga yawan kai hare-hare kwanan nan a wasu sannan Najeriya, musamman a Arewa.
