Ba Dimukura?iyya Ake Yi Yanzu A Najeriya Ba – Na’Abba

Tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya Ghali Umar Na’Abba ya zargi gwamnoni da cewa su ne matsalar Najeriya da ke kassara dimokaradiyya a ?asar.

A hirarsa da BBC ya ce gwamnoni suka haddasa duk wani halin da yanzu Najeriya ta tsinci kanta a ciki.

Duk ana ganin dimokaradiyya a Najeriya wuyanta ya isa yanka, amma tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya na ganin da sauran aiki idan aka yi la’akari da manyan matsalolin da suka dabaibaye dimokuradiyyar Najeriya, a cewarsa saboda rashin dimokaradiyyar cikin jam’iyya da siyasar uban gida da kuma siyasar ?angaranci.

Na’Abba wanda aka za?a ?an majalisar tarayya a jam’iyyar PDP kafin ya koma APC, ya ce yanzu dukkanin manyan jam’iyyun babu wadda take bin tsarin dimokuradiyya.

“Yanzu ba ni da jam’iyya saboda ba dimokuradiyya ake ba, kuma ba a yin za?e.”

“Na janye daga takarar sanata saboda an bukaci dole sai na bayar da kudi a tsayar da ni,” in ji shi.

Ya shaida wa BBC cewa suna shirin kafa sabuwar jam’iyyarsu kuma zai nemi takarar kujerar sanata.

Related posts

Leave a Comment