Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce an samu katsewar lantarki ne a sassan Najeriya sakamakon yadda aka lalata layin samar da lantarkin na Odukpani Ikot Ekpene.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar ranar Lahadi ta ce an samu katsewar lantarkin kusan 400MW, wanda ya haifar da rashin wuta a sassan Najeriya.
An fuskanci katsewar lantarki a sassan Najeriya tun ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce an yi nasarar magance matsalar ta hanyar amfani da wani layin samar da lantarkin da ke Calabar.
Katsewar lantarkin a Najeriya ya haifar da Mummunan koma baya a wajen jama’ar kasa lamarin da ya shafi tattalin arziki.
