Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan tashe-tashen hankula na baya-bayan nan da ake samu a jihar Filato.
A cikin wata sanarwa da Tinubu ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan ya?a labarai, Dele Alake, shugaban ya yi alla-wadai da rikicin wanda ya janyo kashe-kashen rayuka a ?aramar hukumar Mangu da kuma wasu kashe-kashen a jihar Benue.
Ya ce “Ana bu?atar ha?uri da yafiya kan kuskuren da wani ya yi matu?ara ana son samar da ingantacciyar al’umma.”
Ya ?ara da cewa “Abin takaici ne yadda jaririya mai watanni takwas a duniya ta rasa ranta sanadiyyar rikicin da ba ta san komai ba a kai a ?auyen Farin Lamba da ke jihar Filato.”
Ya bu?aci shugabannin al’umma da ?ungiyoyin Jama’atu Nasril Islam da CAN su ha?a hannu domin samar da mafita ga lamarin.
Shugaban ya kuma umarci jjami’an tsaro da su za?ulo duk wa?anda ke da hannu a kashe-kashen domin fuskantar hukunci.
Sannan ya bu?aci gwamnatin jihar ta Filato da ta kai ?aukin gaugawa ga wa?anda lamarin ya rutsa da su.
A farkon wannan mako ne hukumomi suka ayyana dokar hana zirga-zirga a ?aramar hukumar Mangu ta jihar Filato bayan tashe-tashen hankula wa?anda suka yi sanadin rayukan mutane da dama.
