Ronaldo Zai Cigaba Da Buga Lamba 7 A Manchester United

Kungiyar Manchester United ta ce Cristiano Ronaldo zai ci gaba da sanya lambarsa 7 da ya ta fi ya bari a kungiyar.

Dan wasan mai shekara 36 zai ci gaba da sa lambar wadda a baya ya sanya, kuma ya karbe ta ne daga wajen dan wasan Uruguay Edinson Cavani wanda yanzu zai koma sanya lamba 21.

Ronaldo zai ci gaba da atisaye da Reds lokacin da ya kammala killace kansa na kwanaki biyar da aka debe masa.

A ranar Alhamis ne ya koma bayan bugawa kasarsa wasa da ya yi, saboda killace kansa da zai yi.

Dan wasan dama ya saba sa lambar da ke da cikakken tarihi a United kuma muna jaddada cewa zai ci gaba da sanya ta bayan dawowarsa, kamar yadda Manchester ta wallafa a shafinta.

Related posts

Leave a Comment