Babu Wanda Zai Sha Cikin Wadanda Suka Kai Hari Kwalejin NDA – Shugaban Soji

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Hafsan Sojin kasa Laftanan Janar Faruk Yahaya, ya lashi takobin cewa wadanda suka kai hari makarantar Sojojin Najeriya NDA dake Kaduna zasu shiga hannu komin daren dadewa.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kakakin makarantar Soji NDA, Bashir Jajira, ya saki ranar Laraba, 1 ga Satumba, wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

An saki jawabin bayan ziyarar da Babban hafsin Sojin ya kai makarantar ranar Talata, 31 ga Agusta, 2021 domin duba makarantar biyo bayan abinda ya faru na harin ‘yan Bindigar.

Wani sashen jawabin yace: Shugaban Dakarun Sojin ya lashi takobin cewa komin daren dadewa, wadanda suka aikata wannan abin kunyan zasu shiga hannu.”

Harin dai ya janyo cece-kuce inda yan Najeriya sukace abu ya munana tunda har Sojoji basu tsira ba.

Related posts

Leave a Comment