Rikicin Siyasar Kano Ya Dauki Sabon Salo

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Abdullahi Ganduje ya caccaki gungun yan majalisar dokokin tarayya da suka kai kararsa hedkwatar jam’iyyar APC kan zargin yadda yake kama karya a jihar.

Ganduje ya bayyana hakan yayinda ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Jiha inda aka kaddamar da kwamitocin zaben Shugabannin jam’iyyar a matakin Jiha.

An yi wannan taro ne a dakin Africa House dake Gidan Gwamnati jihar. A cewar hadimin Ganduje, Aminu Dahiru, yace maigidansa ya kafa hujjoji daban-daban da suka tabbatar da ba’a yin komai a Jam’iyya ba tare da tuntubar yan tawayen ba.

“Kun gaza yiwa al’ummar mazabunku aiki kuma kuna fuskantar matsala sannan kun fara tuhumata kan matsalolin da kuke fuskanta?”

“Kudin da kuke karba a Abuja al’ummarku basu sha romon ba, sannan kuna daura min laifi?”

Sanata Kabiru Gaya, wanda ke cikin Sanatocin da suka kai karar Ganduje Abuja, ya zame kansa daga lamarin. Ya bayyana cewa ya cire kansa daga cikinsu Shekarau ne saboda ba zai yi fada da gwamnan da ya taimaka masa ya zama Sanata ba.

Sanata Gaya yace ba zai yiwa kansa adalci ba idan ya shiga cikin gungun masu kai karar gwamna. Ya yi kira ga Sanata Shekarau da sauran yan majalisan su baiwa Ganduje hakurin tawayen da suka masa.

Sanatocin dake wakilatar jihar Kano gaba daya da wasu yan majalisar dokokin tarayya sun hadu a gidan tsohon gwamnan jihar Kano dake birnin tarayya Abuja.

Sanatocin sun hada da Kabiru Gaya (APC-Kano ta Kudu), Ibrahim Shekarau (APC-Kano ta tsakiya) da Barau Jibrin (APC-Kano ta Arewa) Mambobin majalisar sun hada da Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Sha’aban Sharada (APC-Kano Municipal), Tijjani Jobe (APC-Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado); Haruna Dederi (APC-Karaye/Rogo) and; Nasiru Auduwa (APC-Gabasawa/Gezawa).

Related posts

Leave a Comment