Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Rikici ya barke a kotun shari’ar musulunci ta jihar Kano yayin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nuna rashin jin da?insa kan yadda lauyoyinsa basu kare shi a gaban kotu.
A karo na biyu shehin malamin ya zargi lauyoyinsa da rashin kareshi idan ana kawo shaida kuma basu ba shi dama ya kare kanshi. An ruwaito cewa Malam Abduljabbar ya roki kotu ta bashi dama ya kare kansa tunda lauyoyinsa basu iyawa.
Mai sharia Ibrahim Sarki Yola, ya yi watsi da bukatar malamin, inda ya koma kan lauyansa, Umar Mohammed, wanda ransa ya baci bisa abinda wanda yake karewa ya yi.
Gwamnati ta gabatar da shaidu Tun da farko, a zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan gwamnati, Farfesa Mamman Lawan Yusufari (SAN), ya gabatar da shaidarsa ta farko. Lauyan ya gabatar da wani mai suna, Adamu Muhammad, mai sana’ar ?inki a Gwale, wanda ya tabbatar da cewa shi ?alibinsa ne mai bibiyar karatunsa.
Adamu ya shaidawa kotu cewa ba ?aya ba kuma ba biyu ba yaji Sheikh AbdulJabbar yana kalamai marasa da?i ga Manzon Allah (SAW). Adamu yace: “Ranar 10 ga watan Agusta, 2019, naje masallacin da yake karatu na Asshabulkhahfi, da kunne na, na ji yana batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a kan aurensa da Nana Safiyya (RA).”
An ruwaito cewa ana cikin sauraron shaidar ne Malam Abduljabbar ya ta shi yana mai cewa kamata ya yi a yanke mai hukuncin kisa. A cewar Shehin Malamin da ace ana zarginsa da cin mutuncin Manzon Allah (SAW) to gara a kashe shi kowa ya huta.
Ya kuma kara da cewa tun a baya ya nemi lauyoyinsa su ba shi dama ya nuna inda maganganun da yake fa?a suke a cikin litattafan Hadithi amma suka ?i.
Ana cikin hakane sai lauyansa, Barista Umar Muhammad ya katse shi da cewa Malamin ya ?auka kamar a kasuwa yake, inda zai iya fa?in abinda ransa ya so. Ya kara da cewa yasan cewa wannan shari’ar tana da hatsari sosai amma ya amsa, sai ga shi ba abinda malamin zai saka masa da shi sai zargi.
Alkali ya ?age sauraron ?ara Da rikicin ya nemi yin ?amari ne, Alkali Yola ya baiwa Shehin Malamin tare da lauyan nasa hakuri, sannan ya umarci Abduljabbar ya daina magana sai an nemi ya yi domin nan a kotu yake. Daga nan sai mai shari’a ya ?age zaman har dai 28 ga watan Oktoba, za’a dawo domin cigaba da sauraron sheda ta biyu.
