Kasafin Kudi: Majalisa Ta Koka Da Kason Da Aka Ware Mata

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, 2021, majalisar wakilan tarayya ta koka da kudin da aka ware mata a kasafin shekara mai zuwa da cewa ya yi kadan.

Da ake tattauna wa a kan kundin kasafin kudin shekarar 2020, Benjamin Kalu wanda shi ne mai magana da yawun ‘yan majalisar wakilai, ya soki kasonsu.

Honarabul Benjamin Kalu yace duk da an kara adadin kudin da ake ba hukumomi da ma’aikatu kai-tsaye, babu canjin da aka samu a kason ‘yan majalisa.

Kalu mai wakiltar mazabar Bende a jihar Abia a majalisar wakilan tarayya yace kason majalisar tarayya bai canza daga abin da aka ba su a shekarar nan ba. Muhawara a kan kasafin kudin 2022 “Wannan ya shafi majalisa saboda an kara kason wadanda ake tura wa kudi kai-tsaye, an samu kari daga N484bn zuwa N768.2bn.”

Mai magana da madadin ‘yan majalisar tarayyar kasar ya koka da cewa akwai lokacin da gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudin da aka gabatar mata. Sai kuma gashi a wannan shekarar babu ko sisi da aka kara a abin da ake ba masu yin dokokin.

‘Amma ku tuna, lokacin da muka nemi mu kashe Naira biliyan 150, sai aka rage kason zuwan Naira biliyan 128”.

“Muna fama da kalubalen kudin canji, da kuma rashin kudin-shiga. Meyasa har yanzu muke a kan Naira biliyan 134?” “Kun san duka-duka nawa ne Naira biliyan 134 a kason kudin da za a tura kai-tsaye.”

Related posts

Leave a Comment