Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Rushe Majalisar Zartarwar Jihar

Rahotanni daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya rushe majalisar zartarwa ta jiharsa, cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya rantsar da kwamishinonin da ya sallama ne a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2019. Gwamnan ya sanar da wannan matakin ne yayin wani taron gaggawa na mambobin majalisar zartarwa da ya kira, wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar dake Lafia ranar Litinin.

Gwamna Sule ya sanar da sallamar kwamishinoni, masu bashi shawara, da manyan masu bashi shawara ta musamman banda wa?anda ke jagorantar ?angaren ayyukan jin kai. Sule ya yi amfani da damar da ya samu wajen gode musu bisa sadaukarwarsu wajen aiki tukuru a lokacin da suke cikin ofis a gwamnatinsa.

Da yake martani a madadin tsofaffin mambobin kwamitin zartarwa, Abdulkarim Abubakar, wanda kafin lokacin shine kwamishinan shari’a ya yi godiya ga gwamna bisa damar da ya basu a gwamnatinsa. Ya kuma tabbatarwa gwamna Sule cewa zai cigaba da samun cikakken goyon bayansu yayin da ake fuskantar babban za?e a 2023.

Wane dalili yasa gwamnan ya ?auki wannan matakin? Wani babban jami’in gwamnatin Nasarawa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace mafiyawancin wa?anda gwamnan ya sallama sun shiga gwamnatin ne bisa shawarar magabata.

Hakan yasa ake zargin suna boye namijin kokarin da gwamnan yake yi a zamanin mulkinsa. Yace: “Ya zama tilas gwamna Sule ya sallamesu domin ya samu damar gina gwamnatinsa yadda yake so.” “Matukar Sule bai ?auki matakin da ya dace ba, to yana iya rasa tikitin takara a karo na biyu.”. “Ina da tabbacin ya yi hakane domin samun cikakken iko a gwamnatinsa yayin da yake kokarin neman zarcewa kan kujerarsa a za?en 2023.”

Related posts

Leave a Comment