Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon ministan Noma Alhaji Mohammed Sabo Nanono ya ce ba abu ba ne mai sauki rike ma’aikatar Noma a kasar ba.
Ya ce ma’aikatu masu zaman kansu na matukar taimaka wa wajen mayar da aikin ma’aikatar mai wahala.
Nanono ya bayyana hakan ne yayin mika al’amuran ma’aikatar ga sabon ministan, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, wanda ya gudana a Abuja.
“A wuri na ba abu ba ne mai sauki. A matsayina na wanda ya taba aiki a ma’aikata mai zaman kanta, dole a rika samun sabanin muradi a ma’aikatun gwamnati a nan da can. Amma a karshe mun fahimci juna da su.
“Muna da babban kalubale a wannan ma’aikatar idon kowa na kan mu. Don tashin farashin kaya sai a ce ma’akatar noma ce, abinci, komai dai aka samu matsala. Duk da haka mun karbi wannan kalubale, amma fatana shi ne wata rana ma’aikatar za ta kasance mai magana da murya daya.”
“Muna da babban kalubale a wannan ma’aikatar idon kowa na kan mu. Dan tashin farashin kaya sai a ce ma’akatar noma ce, abinci, komai dai aka samu matsala. Duk da haka mun karbi wannan kalubale, amma fatana shi ne wata rana ma’aikatar za ta kasance mai magana da murya daya.”
