Ganawa Da Tinubu: Kungiyar Kwadago Ta Janye Shiga Yajin Aiki

Gamayyar ?ungiyar kwadago ta kasa NLC ta dakatar da shiga yajin aikin da ta shirya gudanarwar a fadin ?asar sakamakon cire tallafin man fetur.

Shugaban ha?a?diyar ?ungiyar ?wadago ta TUC Festus Osifo ne ya bayyana haka lokacin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise News da safiyar ranar Alhamis.

Ya ce sun ?auki matakin ne bayan ganawar da shugabbannin ?ungiyar suka yi da shugaban ?asa Bola Tinubu, wanda ya nuna zai duba bu?atun ?ungiyar tare da ?aukar matakai cikin gaggawa.

Kan haka ne ya ce ?ungiyar ta dakatar da gudanar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa a ranar Alhamis.

A ranar Laraba ne dai ?ungiyar ta fara gudanar da zanga-zanga a fa?in ?asar domin nuna ?acin ranta kan matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin ?asar ta yi.

A nata ?angare fadar shugaban Najeriya ta fitar da wata sanarwa cikin daren Laraba, inda a ciki take bayyana irin ci gaban da ta ce an samu sakamakon ganawar shugabannin ?ungiyar ?wadagon da kuma shugaban ?asar a fadar gwamnatin ?asar da ke Abuja.

Sanarwar ta ?ara da cewa shugaban zai yi nazari game da bu?atun da shugabannin ?ungiyar suka gabatar masa a lokacin ganawar, domin dakatar da zanga-zangar da ?ungiyar ke fara gudanarwa a ranar Laraba.

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ?ungiyar ?wadagon cewa matatun mai ta Fatakwal za su fara aiki, nan da watan Disamba mai zuwa, bayan kammala aikin gyara su, da kamfanin mai na ?asar NNPCL tare da ha?in gwiwar kamfanin Maire Tecnimont SpA na Italiya.

Sanarwar ta kuma ambato shugaban ?asar na tabbatar wa shugabannin ?ungiyar cewa zai ci gaba da aiki domin ciyar da ?asar gaba, sannan kuma ya yi kira ga shugabanin da su ha?a hannu da shi domin samar wa ?asar yanayin tattalin arziki mai inganci.

Related posts

Leave a Comment