Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya bada umurnin tura ‘yan mata da yan gidan rawa faggen yaki domin sanyaya zukatan mazajen fama dake yaki da kasar Ukraine.
Wannan na cikin shirin murnar cika shekara guda da fara yakin Rasha da Ukraine.
An umurci kwamandojin su shirya sharholiya wa jami’an Sojojin. Sama da yan mata 100 za’a tura cikin jirage a Donbas inda za’a kwashe kwanaki biyar ana hutu da sharholiya.
Wani jami’in sojan Rasha mai matsayin Kanar ya bayyana hakan a shafin ra’ayi da sada zumunta. Sojan wanda aka yiwa lakabin ‘armoured death’ ya ce: “Za’a shiryawa jarumanmu Casu na musamman tare da yan mata yan rawa, barasa da abinci don nuna godiyanmu bisa bautar da suke wa kasar.”
