Dakarun Soji Sun Hallaka Kwamandan Boko Haram Abu Iliya Da Mayakansa

Dakarun rundunar sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai Tare da hadin gwiwar yan sa kai na CJTF sun murkushe mayakan kungiyar ta’addanci 32 a jihar Borno.

Hakazalika dakarun sojin sun kashe babban kwamandan Boko Haram, Abu Illiya a yayin wani samame da suka kai sansanin yan ta’addan da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

An tattaro cewa dakarun sun cimma wannan nasarar ne a yayin wani zazzafan fatrol da suka kai wasu mabuyar Boko Haram a kauyukan Kayamari, Habasha da Yuwe.

Wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun sun yi karo da yan ta’addan a yayin da suke fatrol a Yuwe wanda ya yi sanadiyar musayar wuta a tsakaninsu. Majiyoyin sun bayyana cewa sojojin sun yi nasarar lallasa mayakan na Boko Haram yayin da sauran suka tsere saboda karfin wuta daga sojojin inda suka yi watsi da kayayyaki da makamansu.

Related posts

Leave a Comment