Ranar Dimukuradiyya: Tinubu Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Zuciya Ga ‘Yan Kasa

A jawabin ranar dimukura?iyya ta bana da ya gabatar kuma ta farko a matsayin sa na shugaban kasa, Alhaji Bola Ahmed Těnubu ya bukaci ‘Yan Najeriya su ha?a hannu da gwamnati wajen ciyar da Najeriya gaba.

Shugaban kasa Těnubu wanda ya jinjina wa Tsohon Shugaban ?asa Buhari bisa sunnanta wannan rana ta 12 ga Watan Yuni a matsayin ranar dimukura?iyya, yace har abada tarihi ba zai manta haka ba.

Shugaban kasar yace tabbas a fili yake tarihin siyasa ko dimukura?iyya a Najeriya ba zai cika ba sai an ambato gwarzo kuma cikakken mai kishin kasa marigayi Chif Moshood Abiola wanda ya yi nasara a zaben shugaban ?asa da aka yi a shekarar 1993 sannan ya rasa ranshi a kokarin ganin dimukuradiya ta tabbata a Najeriya.

“Ba za mu mance gwaraza irin su marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’adua ba wa?anda suka sadaukar da komai nasu domin ganin nasarar wanzuwar mulkin dimukura?iyya a Najeriya”.

“Ba za mu manta gwarzuwa cikin mata ba Marigayiya Hajiya Khudirat Abiola wadda ta rasa ranta a kokarin ganin tabbatuwar nasarar mijinta marigayi Moshood Abiola a matsayin wanda ya lashe za?en da aka yi.

Shugaban ?asa Těnubu ya sha alwashin yin dukkanin mai yiyuwa wajen ganin an saukaka wa ‘yan Najeriya ra?adi da zogin da suke sha sakamakon cire tallafin Mai.
“Za mu bi dukkanin hanyoyin da suka kamata wajen dawo da Najeriya da ‘yan Najeriya cikin hayyacin su.

Daga ?arshe mai girma Shugaban ?asa Tinubu ya bukaci kafatanin ‘yan Najeriya da su nuna kishin ?asa wajen bayar da gudunmawar su ta kawo cigaba ba Najeriya.

Related posts

Leave a Comment