Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta DSS ta ce yanzu haka ta kama tare da tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.
A safiyar yau Asabar DSS ta ce Emefiele ba ya hannunta a lokacin, kafin daga baya ta tabbatar da cewa ya shiga hannun nata a yanzu.
Tun a daren jiya Juma’a wasu rahotanni suka ce jami’an tsaron sun yi awon gaba da shi jim ka?an bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga mu?aminsa.
“DSS na tabbatar da cewa Emefiele, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, yanzu haka yana hannunmu don gudanar da bincike,” a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC sun zargi Emefiele da yun?urin hana su yin nasara a babban za?en da aka kammala a watan Fabrairu saboda tsarin rage yawan kudi a hannun jama’a da ya ?addamar da kuma sauya fasalin kudi na naira.
Kafin haka, DSS ta zargi Emefiele da taimaka wa ta’addanci, har ma aka kai shi kotu kan zarge-zargen.
