?an takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour Peter Obi, ya bi sahun dandazon magoya bayan jamiyyar, inda ya ziyarci shagabannin jamiyyar a helkwatar su da ke Abuja.
Shugaban jamiyyar na kasa wanda ya kaddamar da sabbin yan kwamitin gudanarwa na jamiyyar a karkashin jagorancin Barista Julius Abure, ya bukaci yan kwamitin su sanya rayuwar yan Nijeriya da ma kasa baki daya a sahun farko na dukkan alamurran su.
Peter Obi, ya ce ya kasance a sakatariyar jamiyyar ne musamman don ya ziyarci shugaban ta, ya na mai shan alwashin ci-gaba da yin duk mai yiwuwa don ganin an sasanta matsalolin da jamiyyar ke fuskanta a cikin gida.
Ya ce duk kalubalen da Nijeriya ke fuskanta su na da nasaba ne da rashin inganta rayuwar alumma, musamman bangaren samar da abinci da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da kuma ruwan sha.
Peter Obi ya kara da cewa, yanzu abin da ya rage kawai shi ne tunanin yadda rayuwa za ta iya dorewa kafin wani lokaci, domin babu abin da ya damu yan siyasa illa tunanin zabe na gaba ba zancen rayuwar alumma ba, amma shi a wurin sa, idan jamaa su ka rayu zuwa lokacin zabe sai a yi maganar da ta shafi hakan.
Ya ce abu mai mahimmanci shi ne, fuskantar inda Nijeriya ta dosa tare da tabbatar da cewa ta na murmurawa, to a nan ne jamiyyar Labour za ta iya tagazawa.
A na sa jawabin, shugaban jamiyyar Labour na kasa Julius Abure, ya ce kwamitin gudanarwa na jamiyyar na kasa ya ji dadin ziyarar da dan takarar shugaban kasar da magoya bayan ta su ka kai masu.
Ya ce lokaci ya yi da bangarorin da ba su jituwa da juna sanadiyyar babban taron Nnewi za su hada kai domin tabbatar da samun nasarar jamiyyar a zabe na gaba.
Julius Abure, ya ce taron dai ya riga ya wuce, don haka duk wadanda ke rike da juna a zuciya ana rokon su maida wukar su kube, su hada kai tare da ba su goyon baya a gina jamiyyar a samar da kyakkyawar Nijeriya.
Ya ce ya na da yakinin cewa, matukar aka kai zuciya nesa tare da tunkarar abin da ya shafi ci-gaban Nijeriya haka za ta cimma ruwa.
Shugaban jamiyyar Labour na birnin tarayya Abuja Peter Dugwu da ya shiraya ziyarar, ya ce reshen jamiyyar na birnin tarayya ya na hada hannu da kwamitin gudanarwar jamiyyar domin tabbatar da ganin an yi nasara a zabubbukan kananan hukumomi.
Sa hannun:
OBIORA IFOH
Sakataren Yada Labarai Na Jamiyyar Labour

