Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yi watsi da nadin sabon Sarkin Kontagora, bisa karar da wasu yan takara 46 suka shigar kan zargin murdiya da rufa-rufa da akayi a zaben.
Hakazalika gwamnan ya canza kwamishanan harkokin sarakunan gargajiya. Abdulmalik Sarkin-Daji, wanda ake zargi da murdiyan, da cin amanar aikin shi.
A ranar Lahadi ne aka sanar da babban dan kasuwa Mohammadu Barau-Mu’azu, matsayin sabon Sarkin Kontagora, bayan samun rinjaye a zaben da masu zaben Sarki biyar suka ka?a.
Amma daga sanarwar, sauran yan takara suka fara zanga-zanga inda suka zargi Kwamishana Sarkin-Daji da rufa-rufa, da yin murdiya da magudi.
Sun ce ba’ayi daidato wajen zaben ba saboda Kwamishinan na da wanda yake so. Mika Anache, wanda ya shigar da kara madadin sauran yan takara 46 yace basu yarda da zaben da aka gudanar ranar 19 ga Satumba ba.
Sakamakon wadannan kararraki, Sakataren gwamnatin jihar, Ahmad Matane, a ranar Talata ya bayyana cewar zaben da aka gudanar ya bar baya da kura.
“Saboda nuna cewa gwamnatin jihar ba tada son rai kan wannan zabe, gwamnan jihar ya bada umurnin sake gudanar da zabe.” “Saboda haka, an sauke kwamishanan kananan hukumomi da lamuran sarakunan gargajiya, Barr Abdulmalik Sarkin-Daji daga kujerarsa kuma an mayar da shi ma’aikatar cigaban matasa.”
Ya kara da cewa an nada Emmanuel Umar, sabon kwamishanan kananan hukumomi da lamuran sarakunan gargajiya na wucin gadi.
