Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya a ranar Juma’a ta bayyana cewa kimanin mutane milyan hudu da dubu dari biyu ta tsamo daga cikin matsanancin talauci ta aikin noma cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ministan Noma da raya karkara, Mohammed Mahmoud, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai da aka shirya don murnar ranar abinci ta duniya 2021 a Abuja.
Ya bayyana cewa an samu cimma hakan ne ta hanyoyin tallafi da dama da aka baiwa manoma da yan kasuwan kayan masarufi.
Ya jaddada niyyar Shugaba Muhammadu Buhari na tsamo mutum milyan 100 daga cikin talauci, wanda kowa ya ga hakan ta fuskar noma.
“Ta hanyar shirye-shiryen tallafi da kuma noma da kasuwancin kayan masarufi, mun tsamo jimillar mutum 4,205,576 daga talauci cikin shekaru biyu da suka gabata.” “Za mu cigaba da wannan saboda yana cikin manufofin shugaban kasa a alkawarin da yayi na tsamo yan Najeriya milyan 100 daga cikin talauci cikin shekaru 10.”
A sashen ilmantar da mutane kan harkar noma, Ministan ya ce gwamnati ta horas da manoma, matasa, maza da mata 2,205,576 kan ilmin noma kuma an tallafa musu, kuma wannan shiri na cigaba da gudana.
Ministan ya kara da cewa sashen noma zai cigaba da bada gudunmuwa wajen inganta tattalin arzikin GDP na Najeriya daga 23% zuwa 50% nan da shekaru goma.
