Barazanar Da Muke Fuskanta Ita Ce Kwararowar Boko Haram Arewa Maso Yamma – El Rufa’i

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar mai girma Gwamna Nasir El-Rufai, ya ce yankin arewa maso yamma an shiga rudani ganin cewa akwai yuwuwar ‘yan ta’addan Boko Haram su tattaro komatsansu daga arewa maso gabas, su dawo nan.

Gwamna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i Ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron da gwamnatin jihar Ekiti ta shirya mai suna ‘Fountain Summit’.

A yayin jawabi, gwamnan jihar Kaduna ya ce ya dace dukkan ‘yan Najeriya su damu da lamarin tsaro ba tare da duban yankin da matsalar ta shafa ba. El-Rufai ya kara da cewa, duk da Kaduna ta na fuskantar kalubalen tsaro, masu zuba hannayen jari sun san cewa kadarorin su na tsare.

“Muna da kalubalen tsaro, amma masu zuba hannayen jari sun san cewa kadarorinsu na tsare. Ba mu taba ganin kanun labaran tsaro sun dakile mana hannayen jari ba,” “Amma dole ne mu yi aiki tare wurin inganta tsaro.

“Idan za ku tuna, lokacin Boko Haram ta shafi arewa maso gabas kadai ne. Yanzu babban abun tsoronmu shi ne yadda Boko Haram ke tattarawa suna dawowa yankin arewa maso yamma saboda yadda ake fatattako su daga arewa maso gabas.

“Idan aka fatattake su a yankin arewa maso yamma, ina ku ke tsammanin za su tafi? Can wani wuri. Abu ne da ya dace duk mu damu da shi, ba gwamnatin tarayya da na jihar ba, dukkan fadin kasar nan ya dace mu damu.

“Ka da ku ga abinda ke faruwa a jihar Kaduna ku ce ba matsalar ku ba ce. Wata rana zai zama matsalar ku idan ba a shawo kan shi ba.”

Related posts

Leave a Comment