Mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya taya Asiwaju Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, murnar samun nasarar lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyya mai mulki ta APC.
A cikin wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren watsa labarai na gwamnan ya fitar, na bayyana Ganduje ya ce nasarar da Tinubu ya samu a zaben fidda gwanin alama ce da ke nuna ya samu karbuwa a arewa da ?asa baki daya.
Gwamnan na Kano kuma ya ce nasarar ta Tinubu za ta karfafa jam’iyyar kuma wadanda suka fice daga jam’iyyar ma za su dawo.
“Gagarumar nasarar Asiwaju Bola Tinubu a zaben fidda gwani da aka kammala na jam’iyyar APC ya nuna karbuwa sosai da ya samu a arewa, a matsayinsa na mai hada kan al’umma,” in ji sanarwar. “Wannan matakin na kishin kasa zai hada kan sassan kasar daban-daban.
