Gwamnatin Najeriya ta ce za ta tabbatar da cewa an yi wa jagoran kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu adalci a tuhumar da ake yi masa kan aikata laifuka 11, ciki har da cin amanar kasa da aikata ta’addanci.
A gefe guda gwamnatin ta ce ba za ta kyale duk wanda ta kama da hada baki da shugaban na IPOB wajen kaddamar da hare-hare a kan Najeriya da jama’arta ba, ‘’komai girman matsayinsa’’
Jaridar Vanguard ta rawaito ministan Yada Labarai na Najeriya Lai Mohammed ne ya bayyana matsayin Gwamnatin Tarayyar a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja da safiyar Alhamis.
Ministan ya ce tun shekaru biyu da suka gabata gwamnatin Najeriya ke bibiyar Kanu wanda ke rayuwa ta kasaita a kasashe daban daban, ciki har da zama a manyan hotel hotel na kasaita da kuma yin tafiye tafiye a jirage masu zaman kansu.
