Kaduna: Kotu Ta Dage Shari’ar Zakzaky Zuwa Karshen Wata

Kotun jihar Kaduna, ta sanya ranar 28/07/2021 domin ta yanke hukunci kan shari’ar Zakzaky da gwamnatin jihar Kaduna, wacce ta shafi kimanin shekaru 5 ana gabatarwa.

A zaman da akayi yau wanda shi ne na ?arshe, lauyan Ibraheem Zakzaky Mr. Femi Falana ya bayyana cewa “Dukkan wadanda aka zarga da kashe Kofur Yakubu Dankaduna an gabatar da su a gaban wannan kotu kuma kotu ta sallamesu. Ya ce tunda kotun nan ta sallami wadanda aka zarga da kisan ta yaya za a hukunta wanda ake zargin ya bada umarni?

Ya ce maganar tare hanya kuma ko taro ba bisa izini ba, shima wani abu ne da ya kamata kotu ta sani cewa ba zai shafi wanda ake kara ba. Domin an kama wadanda ake zargi kuma an gabatar da shaidu dukkansu ba wanda ya jingina wannan tare hanya ga Zakzaky.

Ana shi ?angaren Lauyan gwamnati Barista Dari ya ce ana iya hukunta wanda ya taimaka aka aikata laifi ko da an saki wanda ya aikata laifi din. Dari ya nemi kotu da ta yi watsi da bukatar Lauyan Zakzaky.

Bayan kotun ta gama sauraron duka bangarorin Lauyoyin ta sanya ranar 28/07/2021 domin yanke hukunci kan shari’ar.

Related posts

Leave a Comment