Rahotanni daga garin Mina fadar Gwamnatin Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa mafi yawancin ‘yan bindigan da suka addabi yankin arewa daga ?asashen waje suka fito ba ‘yan ?asa bane.
Gwamnan yace ya zama wajibi a kan yan Najeriya su yi iyakar bakin ?o?arin su wajen ganin yan bindiga ba su yi nasara akan su ba, ta hanyar juriya da jajircewa.
Gwamna Bello ya fa?i haka ne yayin ?addamar da ha?akar wakilan jami’an tsaro 1000 na musamman domin tabbatar da an ?u?utar da ?aliban islamiyyar Salihu Tanko, Tegina, ?aramar hukumar Rafi dake Jihar ta Neja.
“Mafi yawancin wa?annan yan bindigan daga wajen Najeriya suke, an ?auko su ne su hana mu zaman lafiya. Wannan ba ya cikin al’adar fulani su aikata irin wa?annan munanan ayyukan.”
An ruwaito cewa jami’an tsaron da gwamnan ya ?addamar sun ?unshi wakilai daga yan sanda, sojoji, yan sa kai da jami’an NSCDC.
Hakazalika Gwamna Bello Ya gana da iyayen ?aliban da aka sace ya gana da iyayen ?alibai 136 da yan bindiga suka sace a makarantar Salihu Tanko dake Tegina a fadar Sarkin Kagara,
Gwamnan ya jajanta musu kan lamarin, sannan ya ro?i su cigaba da hakuri, domin gwamnatinsa zata yi duk abinda ya kamata wajen ganin ?aliban sun dawo cikin ?oshin lafiya. Yace: “Duk da mun cire maganar biyan ku?in fansa, amma lokaci yayi da gwamnati zata ?auki duk matakin da ya kamata domin magance harin yan bindiga.” “?arayin ba su da mutunci, Amma gwamnati zata ?au mataki a kan su.
