Rasha Ta Gindaya Sharuddan Kawo Karshen Yaki Da Ukraine

Rahotannin dake shigo mana daga kasar Rasha na bayyana cewar Turkiyya ta fitar da bayani dalla-dalla kan yarjejeniyar zaman lafiyar da Rasha ta gabatar da nufin tsagaita wuta a yakin da ake yi a Ukraine.

Sanarwar na zuwa ne bayan Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya tattauna ta waya a yau da Shugaba Putin na Rasha.

Dole ne Ukraine ta amince cewa ko a nan gaba ba za ta shiga cikin ?ungiyar ?awancen tsaro ta NATO ba.

Sannan Rasha ta bu?aci cewa Ukraine ta amince yankin Crimea da Rasha ta ?wace a 2014 da wasu ?angarori na gabashin Ukraine ?in za su zamo a ?angarenta.

Shugaba Putin ya shaida wa Mista Erdogan cewa wadannan batutuwa za a cimma su ne idan sun ha?u gaba da gaba tare da Shugaban Ukraine, Zelensky.

Related posts

Leave a Comment