Rahoton dake shigo mana daga Lafiya babban birnin jihar Nasarawa na bayyana cewa Yan bindigan da suka yi garkuwa da kwamishinan ya?a labarai, al’adu da yawon bu?e ido na jihar Nasarawa, Lawal Yakubu, sun rage yawan ku?in fansa zuwa miliyan N20m.
An ruwaito cewa yan bindiga sun yi awon gaba da kwamishinan ne a gidansa da ke Nasarawa Eggon, hedkwatar karamar hukumar Nasarawa Eggon ranar Litinin.
Bayanai sun nuna cewa an ?ara tura dakaru na musamman daga Barikin Doma, hedkwatar ?aramar hukumar Doma,
Wani ?an gidan su kwamishinan, wanda ya nemi a ?oye sunansa, ya fa?a wa yan jarida cewa masu garkuwan sun sake kiran waya ranar Alhamis da ?arfe 10:30 na safe suka bu?aci miliyan N20m.
