2023: Hikima Ta Sa Muka Hada Musulmi Da Musulmi – Shugaban APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban jam’iyyar APC na ?asa Sanata Abdullahi Adamu, ya ce takarar mabiya addini ?aya da jam’iyyarsa ta yi shi ne abinda yan Najeriya ke bukata a halin da ake ciki.

Da yake hira da BBC Hausa, Adamu ya bayyana cewa takarar Musulmi da Musulmi, wata babbar dabara ce ta APC domin ta lashe za?en 2023 ?a ke tafe.

Kamar yadda jama’a suka sani dai ?an takarar shugaban ?asa ?arkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya za?i tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.

“Duba da yanayin da Najeriya ke ciki, ba zaka iya gamsar da kowa ba. Haka Demokara?iyya ta kunsa kowa na da yancinsa amma a wajen mu, musulmi da musulmi ne ya dace da Najeriya a yanzu.”

“Amma ba zamu yi ?asa a guiwa ba, zamu yi aiki tukuru don fahimtar da ?an Najeriya su goyi bayan tikitin Tinubu da Shettima. Kowace jam’iyya na da dabarunta, mu kuma wannan ce dabarar da muke ganin zata ?ulle mana.

Related posts

Leave a Comment