Fidda Gwani: Osinbajo Ya Shiga Rudani Bayan Shan Kaye

Mataimakin Shugaban ?asa Osinbajo ya yi warwas a za?en fidda gwani na jam’iyyar APC inda tsohon ubangidansa kuma jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya samu kuri’u 1,271 kuma ya tabbata ‘dan takara shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa a APC.

Kafin zaben, masu nazarin al’amurra sun yi ittifakin cewa ta yiwu Osinbajo ya sha wuya tunda a bayyane ya kalubalanci tsohon ubangidansa, jigon siyasar kasar Yarbawa kuma ‘dan takarar da yayi nasarar samun tikitin APC.

Kin goyon bayansa a bayyane da Buhari ya yi A yayin da ya ke a bayyane cewa Osinbajo na neman kujerar ne tare da amfani da sunan ubangidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, babu alamar goyon baya ko kadan daga shugaban kasan kan burin mataimakinsa.

Lalacewar shirin tsayar da ‘dan takarar yarjejeniya Bayan shirun da Buhari yayi, batun tsayar da ‘dan takarar yarjejeniya ya taso wanda da an yi hakan zai karfafa burin mataimakin shugaban kasan.

Duk kokarin da shugabancin jam’iyyar ya yi wurin tsayar da ?an takarar yarjejeniya, ya tashi a kawai. A yayin da masu lura ke ta hasashen cewa Osinbajo ne zabin Buhari, saboda biyayyar da ya ke masa, Abdullahi Adamu, shugaban APC ya sanar da cewa Ahmed Lawan ne zabin Buhari wanda hakan yasa Osinbajo ya fara cire rai.

A fili yake a yanzu Osinbajo ya shiga matukar ru?ani dangane da sanin makomar siyasar shi, bayan jayayya da ubangidan shi da ya yi da kuma juya mishi baya da Buhari ya yi.

Related posts

Leave a Comment