Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufai, ya ce nasarar da jam’iyyar PDP ta samu na lashe zabe a akwatinsa ya nuna cewa APC bata yi magu?i ba da na’urar zabe na zamani.
A ranar 4 ga watan Satumba, hukumar zabe na jihar Kaduna, KADSIECOM, ta yi zabe ta hanyar amfani da na’urar mai amfani da lankarki.
Kafin wannan lokacin, Jihar Kaduna ce ta farko da ta fara amfani da wannan sabon tsarin zaben na zamani a Nigeria. Sai dai, jam’iyyar APC ta sha kaye a akwatin El-Rufai yayin zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar a jihar.
” Idan da mun yi magudi ba zan fadi a akwati na ba, El-Rufai Da ya ke magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin din Channels a ranar Litinin, El-Rufai ya ce sakamakon zaben ya nuna cewa jam’iyyar mai mulki ba ta yi magudi ba wurin tsara na’urar zabukan.
Ya kuma ce sakamakon ya nuna babu rabuwan kai a jihar sannan, ya kara da cewa hakan hujja ne da ke nuna mutane sun fara yin zabe bisa aikin da wadanda suka zaba suka yi.
“Wadanda suka kai rahoto cewa an sauya tsarin na’urar don yin magudi sun ji kunya a lokacin da aka ruwaito cewa APC ta sha kaye a akwati na. Mutane na dariya cewa na sha kaye a akwati na amma demokradiyya ce ta yi aiki.”
“Ba suna na bane a takardan zaben don haka ba hujja bane a kai na, hujja ne kan kansilar da shugaban karamar hukuma.
Rashin nasara a akwatin zabe na ya nuna cewa ba mu yi magudi ba ko lalata na’urar, ba mu yi wa hukumar zabe mai zaman kanta na jihar mu katsalandan ba kuma komai ya tafi dai-dai.
“Sakamakon zaben kawo yanzu ya nuna kan mutanen mu ya hadu dama shine abin da muke aiki a kai. Muna son mu canja yadda wasu ke dauka cewa jam’iyyar PDP na wani bangare ne a jihar, wani sashin kuma na APC.
