Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Babban Malamin addinin Islama mazaunin jihar Sheikh Ahmad Gumi, ya yi ikirarin cewa farmakin da sojoji ke kaiwa kan ‘yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma ba zai magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.
Malam Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ta shafinsa na Facebook, yayin da yake mayar da martani kan nasarorin da sojoji ke samu a kan ‘yan bindiga a dazuzzukan Zamfara.
Dole ne a ilmantar da ‘yan Najeriya idan ana son Ta’addanci ya kare Sanarwar, mai taken: ‘Zamfara: The Flaring of Crisis’, ta jaddada cewa matakin soji kan masu aikata miyagun laifuka “ba mafita bane ko hikima”.
A cikin sanarwar, Gumi ya bayyana yadda gwamnati ke tafka asara wajen kashe kudade don sayen makamai da jiragen yaki kuma babu wani sauyi a yakar ‘yan bindiga, wanda a cewarsa, zai durkusar da tattalin arzikin kasar.
Sanarwar ta ce: “Abin takaici, wannan ba mafita bane ko hikima. Lokacin da ba ku da ikon kayayyakin aikin dakile tashin hankali, to tattaunawa tana da ikon warware rikici. “Wannan shi ne abin da Majalisar Dinkin Duniya ke nufi. watau kudurin daidaita rikice-rikice.
Abin da muke gani ya wuce masu ‘yan ta’adda da ta’addanci kawai, eh yana iya farawa kamar haka amma kamar kowane rikici, yana da sarkakiya.”
Dr Gumi ya kara bayyana cewa, ya tattauna da ‘yan bindiga da dama kan yadda za su mika wuya da kuma tattaunawa dasu. Hakazalika, ya bayyana cewa, ya gana da gwamnoni da shugabanni da yawa, sun kuma tabbatar da zabin tattaunawa da ‘yan bindiga fiye da daukar matakan soji.
