Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana fatan wanda ke da “kyakkyawar zuciya” kamar Shugaba Muhammadu Buhari zai fito a matsayin wanda zai maye gurbinsa a 2023.
Gwamna Umahi ya fadi hakan ne duk da cewar ya ce ya yi wuri sosai da za a shiga harkokin siyasar 2023 kamar yadda ya lura cewa hakan zai zama shagala a bangaren shugaban kasa da gwamnonin jihohi.
Gwamna Dave Umahi ya nuna fatan cewa Allah zai sake bamu shugaban kasa kamar Buhari a 2023. Gwamnan, wanda ya amsa tambayoyi daga manema labarai bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Litinin, ya kuma lura cewa membobin jam’iyyun siyasa daban-daban daga Kudu maso Gabas suna aiki a cikin jam’iyyunsu don tabbatar da ganin cewa an mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin.
