Wasanni: Chelsea Ta Lallasa Arsenal Da Ci 2 Da Nema

Kungiyar kwallon ?afa ta Arsenal tayi rashin nasara a gasar Firimiya bayan da Chelsea ta lallasa ta har gida da ci 2 da 0.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci Lukaku ya zura kwallo ta farko zuwa kusa mintuna 36 kuma James ya ?ara ta biyu a ragar Arsenal.

Wannan shine wasa na biyu a gasar firimiya na kakar bana wasa na farko ma Arsenal din rashin nasarar tayi da ci 2 da 0.

Har ila yau dai a ranar 28 ga wannan watan na Ogusta Arsenal din zata ziyarci kungiyar kwallon ?afa ta Manchester City har gida, sai dai tun yanzu har yan Arsenal sun karaya.

Rashin nasarar da Arsenal din tayi a yau ya saka ta koma matakin na 19 a kan jadawalin tebirin Firimiya, ita kuwa Chalsea ta koma matakin na farko.

Related posts

Leave a Comment