Injiniya Yabagi Sani, masani kan harkar makamashi ya ce matsalar rashin wuta a Najeriya ta zama abin damuwa.
Ya ce gwamnati ta saka isasshen ku?in da ya kamata wajen inganta ?angaren wutar lantarki.
“Halin da aka shiga da aka cire tallafin mai, gwamnati ba za ta iya fitowa ta ce an cire tallafin da ake bayar wa a ?angaren wutar lantarki ba.”
“Ke nan gwamnati ta kasa domin ba ta da ku?in kuma rashin ku?in ya sa abin da ke bu?ata domin yin gyara a ?angarorin samar da wutar lantarkin.” in ji shi.
Masanin ya ce har yanzu Najeriya ba ta samar da rabin ?arfin wutar da ya kamata ta rika samarwa ba, kasancewar a yanzu tana iya samar da megawatt dubu 13 kawai.
“Abin da muke bu?ata da zai samar da isasshiyar wuta a Najeriya ya kai megawatt dubu 25.” kamar yadda ya ce.
