Uwargidan shugaban ?asa Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi don ?ara shiga harkar noma, inda ta ce ?asar za ta iya samarwa kanta isasshen abinci.
Remi ta fa?i haka ne a lokacin da ta kar?i bakuncin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar ?inkin Duniya, Amina Mohammed a ofishinta ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja.
Uwargidan shugaban ?asar ta bayyana cewa, ?ullo da shirye-shirye dban-daban da gidauniyarta ta Renewed Hope Initiative ta yi, musamman a fannin noma, samar da aikin yi, ilimi, lafiya da jin da?in jama’a, duka ta yi shi ne don ?ara karfafa irin ?o?ari da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi.
“Shugaban ?asa ya ?auki matakan da suka dace. Wa?annan matakai za su taimaka mana wajen gina Najeriya. Ya kamata mu zama masu gaskiya dangane da albarkatun da Allah ya ba mu,” in ji Remi.
Ta kuma nanata bu?atar zaburar da matasa wajen yin tunanin da ya dace a kan ?asar.
