An Datse Layukan Sadarwa A Jihar Katsina

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar an toshe layukan sadarwa a wasu sassa na jihar kusan mako guda kenan bayan an toshe na jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar.

Mai bai wa gwamnan Katsina shawara a kan harkokin tsaro Ibrahim Ahmed Katsina ne ya tabbatar wa BBC da batun katse layukan inda ya ce an ?auki matakin ne domin inganta tsaro a jihar.

?ananan hukumomin da lamarin ya shafa sun ha?a da Funtua da Bakori da Jibiya da Malumfashi da Faskari da Batsari da ?anmusa.

Sauran kuwa su ne Sabuwa da Kankara da Dutsinma da Kurfi da Safana da ?andume.

A cewar Ibrahim Kastina, ya zama wajibi gwamnatin Katsina ta ?auki wannan mataki, domin hana ?an bindigar da ke Zamfara gangarawa Katsina su ci gaba da amfani da waya da gudanar da harkokinsu.

Akasarin ?ananan hukumomin da aka toshe hanyoyin sadarwar na makwabtaka da Zamfara da kuma Kaduna sakamakon yadda yanayin tsaro ya ?ara ?amari a jihohin, in ji Ibrahim Katsina.

“Ma?asudin wannan mataki shi ne hana ya?uwar ta’addanci, duk inda muka ga yana ya?uwa to za mu toshe amma a halin yanzu wa?annan ?ananan hukumomin da abin ya yi ?amari aka toshe domin a samu cin ?arfin abin kuma a taimaka wa jami’an tsaro su samu gudanar da aikinsu cikin sau?i”, a cewarsa.

Ya kuma bai wa jama’ar ?ananan hukumomin da abin ya shafa ha?uri inda ya ce an ?auki wannan matakin ne domin jama’a su samu sau?in wannan lamari.

A makon nan ne dai aka yi ta ya?a wata takarda a shafukan sada zumunta inda takardar ke cewa hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta bayar da umarni a rufe hanyoyin sadarwa a Katsina.

Sai dai gwamnatin Katsinar ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Abdu Labaran ya fito ya ?aryata batun inda ya ce shugaban NCC ya tabbatar wa gwamnatin Katsina da cewa takardar ta bogi ce.

Related posts

Leave a Comment