Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya roki ‘yan Najeriya wurin kimanta gwamnatin Bola Tinubu a kasar.
Shettima ya bukaci ‘yan kasar su yiwa Tinubu adalci yayin kimanta gwamnatinsa duba da kokarin da yake yi wurin daidaita kasar.
Shettima ya bayyana haka ne a ran Juma’a 28 ga watan Yunin 2024 yayin wani babban taro a Abuja,
Tsohon gwamnan Borno ya ce Tinubu na aiki ba dare ba rana domin ganin ya inganta kasa
. Ya kuma ba da tabbacin cewa Tinubu yana iya bakin kokarinsa wurin tabbatar da komai ya daidaita a kasar, kamar yadda VON ta tattaro.
Kashim ya magantu kan matsalar tattalin arziki Ya ce matsalar tattalin arziki ba iya Najeriya ba ne kadai inda ya ce duk duniya ana fama da wannan matsalar.
Har ila yau, Shettima ya ce bai taba ganin lokacin da Najeriya ta samu shugaba mafi kwarewa mai kishin kasa irin yanzu ba. Shettima ya roki ‘yan Najeriya da su ba shi dukkan gudunmawa da goyon baya domin samun abin da ake nema.
Har ila yau, ya bayyana irin shirin da Tinubu ke yiwa kasar a matsayinsa na kwararren shugaba mai hazaka da hangen nesa.
