Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bai hana sabon shugaban ?asar Bola Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba.
Cikin wani sa?o da mai magana da yawun tsohon shugaban Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa ta twitter ya ce, labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta, wa?anda ke cewa Buharin ya nemi Tinubu da kada ya binciki jami’an gwamnatinsa, labarai ne na ?anzon-kurege.
Gabanin babbar salla ne Bola Tinubu ya gana da Buhari a wata ziyara da ya kai gidansa da ke Landan lokacin wata ziyarar ta ?ashin ?ai da Tinubun ya kai Landan bayan taron harkokin ku?i na duniya da ya halarta a birnin Paris.
To amma Mallam Garba Shehu ya ce a lokacin ziyarar Buhari da Tinubun ne kawai suka gana babu wani mutum a ?akin da suka gana, dan haka babu wanda ya san me suka tattauna.
