Na Rantse Da Allah Buhari Rahama Ne Ga ‘Yan Najeriya – Sabon Minista

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sabon karamin ministan ayyuka da gine-gine, Mu’azu Sambo, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki hanyar da ta dace domin bunkasa ababen more rayuwa a kasar.

Sabon Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, sannan ya samu tarba daga sakataren din-din-din, Babangida Hussaini, da ma’aikatan ma’aikatar.

Sambo ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya, wadanda ke shakka a kan iyawar Buhari za su gane muhimmancinsa ne bayan gwamnatinsa ta kare, a wannan lokacin ne za su farga su fahimci Buhari rahama ne ga ‘yan Najeriya.

“Shugaban kasa alkhairi ne ga kasar nan. Ina kara fada cewa masu shakku ba za su gane hakan ba har zai shugaban kasar ya tafi. Amma wasunmu da suka san cewa ci gaban zamantakewa da tattalin arziki yana da nasaba da dimbin ayyukan samar da ababen more rayuwa, mun san cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi hanyar da ta dace.”

Ya bayyana cewa, samar da ababen more rayuwa na da muhimmanci ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kowace kasa. Hakazalika ya yi misalai da kasashen Sin da Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin kasashe masu gasa saboda zuba jarin da suka yi na samar da ababen more rayuwa.

Ya bayyana cewa zai cimma hakan a tsakanin lokacin da zai kasance a ma’aikatar don taimakawa shugaban kasar wajen barin wasu tarihi a bangaren ci gaban more rayuwa a fadin kasar.

Related posts

Leave a Comment