Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani lauya kuma tsohon sakataren labaran kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Benin, Douglas Ogbankwa, ya bayyana cewa duk mutumin da ya taba matarsa ba yadda ya kamata ba na iya fuskantar laifin lalata da matarsa ma’ana ya aikata fyade.
Ogbankwa ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a ranar Alhamis kan ko yana iya yiwuwa mace ta zargi mijinta da laifin aikata fyade a Najeriya, duba ga al’adarmu.
Ya ce kafin a kafa dokar hana cin zarafin jama’a (VAPP) a wasu jihohin tarayya, baya bisa ka’idar doka a zargi miji da laifin aikata lalata da matarsa, rahoton 21stcenturychronicle. Lauyan ya ce hakan ya samo asali ne saboda wasu kebabbun abubuwa da dokar hukunta masu laifi ta kafa a wasu sassan kasar, wanda ya hana a zargi miji da yi wa matarsa fyade.
Sai dai kuma, ya ce bayan kafa dokar VAPP, lamarin ya sauya sosai kuma a yanzu ana iya kama miji da laifin yin fyade ga matarsa koda kuma ta hanyar tabin da ake ganin baya bisa ka’ida ne. “Kafin zuwan dokar VAPP a wasu jihohi, ba za a iya kama miji da laifin fyade da matarsa ba. “Hakan ya kasance ne saboda ware shi da dokar aikata laifuka ta yi a jihohin Kudu da kuma dokar Penal Code a jihohin Arewa.
“Doka ta tanadi cewa za a iya yin fyade ne kawai ga wacce take ba matar mutum ba. “A yanzu dokar VAPP ta samar da kafar da ake kira fyade a tsakanin ma’aurata, wanda zai iya zama fyade ga miji ko mata. Yanzu an rarraba wannan a matsayin cin zarafin mutane.” Lauyan ya ce wannan ci gaban ya kuma haifar da raguwar shaidar da ake bukata don tabbatar da fyade.
