Na Kagara Na Bar Mulkin Najeriya – Buhari

Shugaban ?asa Muhammadu buhari ya ce ya ?agara ya mika ragamar mulkin kasar ga wanda zai gaje shi saboda wahalar mulkin da yake sha.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki da wasu ’yan majalisa lokacin da suka kai masa ziyarar Sallah a gidansa da ke Daura a Jihar Katsina ranar Litinin.

“Nan da badi warhaka, wa’adin mulkina na shekara takwas ya zo karshe,” inji shi.

Buhari ya kuma shaida musu cewa kusan tsawon shekara guda ke nan bai ziyarci gidan nasa na Daura ba saboda yanayin ayyuka.

Sai dai ya ce da zarar wa’adin mulkin nasa ya kare, a Daurar zai koma ya tare ba a Kaduna ba.

Shugaban ya kuma yi kira ga ?ungiyar malaman Jami’o’i ASUU da su janye yajin aikin da suka shafe watanni suna yi.

Ya bayyana damuwa kan tasirin yajin aikin ga makomar ilimi da ci gaban Najeriya. Yana mai cewa “yajin aikin ya isa haka nan.”

Ya ce duk da ya fahimci bu?atunsu, amma za a ci gaba da tattaunawa yayin da ?alibai ke ajin karatunsu.

Related posts

Leave a Comment